Isa ga babban shafi
Afrika

Kotu ta zargi Isabel Dos Santos

Babban mai gabatar da kara a kasar Angola ya sanar bayyana cewa kudaden da Isabel Dos Santos yar tsohon Shugaban kasar Angola, ta yi amfani da su wajen zuba jari a kasar Fotugal, na daga cikin milyoyin daloli da ta wawure daga kamfanonin kasar ta Angola.

Isabel Dos Santos, yar tsohon Shugaban kasar Angola
Isabel Dos Santos, yar tsohon Shugaban kasar Angola REUTERS/Toby Melville/File Photo
Talla

Babban mai gabatar da kara a Angola, Helder Pitta Gros,ya bayyana cewa yana da yekini kudaden da Isabel dos Santos ta yi amfani da su domin gudanar da harkokin kasuwancinta da su a Fortugal kasar da ta yiwa Angola mulkin mallaka, sun fita daga kasar ba bisa ka’ida ba.

Wannan zargin na zuwa ne, kwana guda bayan Dos Santos, attajira ‘yar tsohon shugaban kasar Angola, ta sha alwashin cewa a shirye take ta yaki abin da ta kira" yaudara da kuma zarge-zarge, na cewa ta wawure kudaden masana'antun man fetur da lu'u-lu'u da kuma bankunan kasar zuwa Lisbon.

Masu gabatar da kara na Angola na zargin Dos Santos da almubazzaranci da kuma karkata makudan kudaden kamfanin man fetur din kasar daga kamfanin Sonangol, da ta jagoranta lokacin mulkin mahaifinta.

Tuni Bankin Eurobic na kasar Fortugal ya sanar a ranar Laraba cewa Dos Santos ta sayar da kason hannun jarin ta ga bankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.