Isa ga babban shafi

Senegal ta haramta zanga-zanga da katse Internet bayan da Amurka ta bukaci a gudanar da zabe

Hukumomi a Senegal sun haramtawa ƴan hamayya gudanar da zanga-zanga ranar Talata a yayin da Amurka ta bi sahun masu kira ga Shugaba Macky Sall ya gudanar da zabe sannan ya mika mulki ga wanda ya yi nasara.

Masu zanga zanga a Senegal
Masu zanga zanga a Senegal © AP / Stefan Kleinowitz
Talla

Mutum uku ne suka mutu tun lokacin da aka soma zanga-zanga a kasar bayan Shugaba Sall ya dage zaben da ya kamata a gudanar ranar 26 ga watan Fabrairu zuwa watan Disamba.

A yayin da kasashen duniya ke ci gaba da matsa lamba kan Shugaba Sall don ya gudanar da zabe, wata gamayyar kungiyoyin fararen-hula da addinai da masana mai suna Aar Sunu Election (Dole mu kare zaɓenmu) ta yi kira a gudanar da zanga-zanga in Dakar.

Sai dai ta janye zanga-zangar har sai ranar Asabar, tana mai cewa hukumomin birnin Dakar sun hana ta yin gangamin suna masu cewa matakin zai kawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa.

An ga tarin jami'an ƴan sanda da aka jibge a wuraren da aka tsara gudanar da zanga-zangar domin tabbatar da ganin b ata gudana ba.

Hukumomi sun katse kafofin sadarwa na yana gizo a karo na biyu tun da Shugaba Sall ya sanar da dage yin zaben.

Ma'aikatar sadarwa ta ce ta dauki matakin ne saboda "masu yada bayanan kiyayya wadanda tuni suka janyo zanga-zanga".

Amurka da Faransa sun jaddada kira ga Shugaba Sall ya gudanar da zabe kamar yadda ya yi alkawari.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken "ya yi magana da shugaban kasar ta Senegal da safiyar nan inda ya jaddada fargabar game da halin da ake ciki a can sannan ya bayyana masa karara cewa muna so a gudanar da zabe kamar yadda aka tsara. Ya kuma ci gaba da cewa suna so a gudanar da shi nan ba da jimawa ba, a cewar kakakin Ma'aikatar Wajen Amurka Matthew Miller a hirarsa da manema labarai in Washington.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.