Isa ga babban shafi

Ana zargin jami'an sa kai na jihar Zamfara sun hallaka babban limamin Mada haka siddan

Kisan babban limamin masallacin juma’a na karamar hukumar Mada dake jihar Zamfara ta arewacin Najeriya Alhaji Abubakar Hassan Mada ya tayar da kura a jihar, bayan da aka zargi dakarun tsaro da gwamnatin jihar ta kaddamar watannin baya.

Jami'an tsaron sa-kai na CPG a jihar Zamfara dake Najeriya.
Jami'an tsaron sa-kai na CPG a jihar Zamfara dake Najeriya. © Daily Trust
Talla

Wani ganau daga kauyen da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa manema labarai cewa dakarun sun kama babban limamin ne ranar Lahadin da ta gabata a kofar gidan sa.

“Mutanen sun zo akan mashina, kuma da isowar su suka bukaci limamin ya hau mashin daya daga cikin wanda suka zo da su sassan suka tafi” Inji ganau din.

Guda daga cikin iyalan mamacin da shima ya bukaci manema labarai su sakaya sunan sa, ya ce lokacin da suka sami labarin kamun, basu damu ba kasancewar sun dauka kawai an tafi da shi ne a dan yi bincike a dawo da shi, amma kawai suka sami labarin mutuwar sa.

“Mutanen sun yanka gawar sa tamkar rago, wannan abin takaici ne kuma bamu taba ganin makamancin wannan tashin hankali a kauyen nan ba, wane dalili ne zai sa a yanka babban limami a irin wannan hanya ta rashin tausayi” Inji Guda daga cikin iyalansa.

Jamar kauyen na Mada sun shaidi limamin a matsayin mutum mai shiru-shiru mara son hayaniya, kuma ba’a taba samun sa da laifin hannu a ta’addanci ba.

Ko da jaridar Daily Trust da ake bugawa a Najeriya ta tuntubi shugaban rundunar tsaron ta jihar Zamfara Kanal Rabi’u ‘Yandoto ya tabbatar da faruwar lamarin sai dai ya ce yayi mamakin kisan limamin, kuma tuni aka kama mutane biyu daga cikin wadanda suka kama limamin tare da kashe shi.

Kanal ‘Yandoto ya ce wannan ba shi ne karon farko da ake samun hannun dakarun na Zamfara da aikata kisa a yayin aiki ba, sai dai ya ce tuni suka fara gudanar da bincike kan mutanen da aka kama din kuma da zarar an kammala za’a mika su hannun hukumomin da suka dace.

Ko da aka tambaye shi dalilin kamun babban limamin ya ce sam baya cikin mutanen da rundunar ke nema kuma ba’a aika dakarun su kama shi ba, don haka su kadai suka san dalilin da ya sa suka yi gaban kansu wajen kama shi da kuma kisan sa.

A cewar sa, dokar da ta kafa su ta haramtawa jami’I daya ya yi gaban kansa wajen kama mai laifi ko kuma hukunta shi har sai ya samu umarni daga shalkwata don haka wannan ma kadai kuskure ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.