Isa ga babban shafi

Farashin kayan abinci ya karu a Najeriya-NBS

Rahoton hukumar kididdiga ta Najeriya ya nuna cewa farashin kayayyaki ya karu zuwa kaso 31.70, a watan Fabrariru idan aka kwatanta da kaso 29.90 da aka gani a watan Janairun da ya gabata.

Wasu mata kenan da ke cinikayya a wata kasuwa da ke yankin Afirka
Wasu mata kenan da ke cinikayya a wata kasuwa da ke yankin Afirka © guardian
Talla

Wannan na nuna cewa an sami karin kaso 1.80, cikin wata guda kachal.

Bayanan da ke kunshe cikin rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu karin farashin kayayyakin abinci matuka da gaske a watan Fabarairun da ya gabata, idan aka kwatanta da watan Fabarairun bara.

Wannan dai tamkar ba wani sabon abu ne a Najeriya ba, la’akari da yadda ‘yan kasar ke kokawa game da tsadar kayayyakin masarufi, lamarin da ke tsananta yanayin rayuwar yau da kullum.

Bayanai sun nuna cewa Najeriya bata taba tsintar kanta cikin irin wannan yanayi na tsadar kayan masarufi ba, al’amarin da ya fara tun bayan da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta janye tallafin man fetur.

Tsadar farashin dala da rugurgujewar darajar Naira ya kara bada gudunmowa wajen jefa ‘yan kasar cikin matsaloli da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.