Isa ga babban shafi

Lokaci yayi da EFCC zata fara kame masu taimakawa 'yan ta'adda da kudade-Rundunar sojin Najeriya

Rundunar sojin Najeriya ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC da ta bibiyi wadanda ke da hannu wajen daukar nauyin ta’addanci a kasar tare da chafke su.

Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa © Sawaba Radio
Talla

Da yake jawabi hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ya ce lokaci yayi da ya kamata hukumar EFCC ta fara amfani da karfin da doka ta bata wajen kama mutanen da ke da hannu a taimakawa masu ta’addanci da kudade.

Yayin da yake karbar bakuncin shugaban hukumar ta EFCC Musa, ya ce kamo wuyan masu taimakawa ta’addanci da kudade shine babban abinda zai kawo karshen hare-haren a Najeriya, kasancewar ayyukan laifin basa tafiya idan babu kudi.

Musa ya kuma jadadda cewa rundunar sojan Najeriya ba ta goyon bayan cin hanci da rashawa, kuma ba zata laumunci shigar sojoji cikin rashawa ba, don haka rundunar zata baiwa EFCC duk hadin kan da take bukata.

A nasa bangaren, Ola Olukoyede shugaban hukumar EFCC a Najeriya ya ce babu wata hukuma da bata da gudunmowar da zata baiwa Najeriya a fannin yaki da rashawa ba, don haka ya zama wajibi jami’an tsaro su san da wannan.

Ya kuma koka kan yadda ake samun cin hanci tsakanin jami’an tsaro, yana mai alakanta hakan da karuwar matsalolin tsaro a wasu lokutan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.