Isa ga babban shafi

Maniyyatan Najeriya sun nemi NAHCON ta mayar musu kudadensu

Maniyyatan Najeriya, sun bukaci Hukumar Alhazan kasar NAHCON da ta mayar musu da kudadensu na aikin hajjin da suka biya, biyo bayan karin kusan naira miliyan biyu da aka musu na tafiya kasa mai tsarki.

Yadda al'ummar musumi ke dawafi a Ka'aba, yayin aikin Hajjin shekarar 2023.
Yadda al'ummar musumi ke dawafi a Ka'aba, yayin aikin Hajjin shekarar 2023. AP - Amr Nabil
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyoyin gamayyar kungiyoyin farar hula na kasar, suka yi kira ga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu da ya ceto maniyyatan kasar, la’akari da halin matsin tattalin arzikin da ake ciki.

A ranar Lahadi ne, NAHCON ta sanar da cewa an kara sama da naira miliyan daya da dubu 900 na kudin aikin hajjin bana ga maniyyatan da ke shirin tafiya kasar Saudiyya sauke faralli, saboda matsalar karyewar darajar kudin kasar.

Darajar kudin Najeriya ta fuskanci koma baya a kan farashin dala a ‘yan kwanakin nan, kodayake a halin yanzu an fara ganin farfadowar darajar kudin kasar, sakamakon matakin da babban bankin CBN ya ce ya fara dauka na shawo kan matsalar.

A ranar 29 ga Maris ne, NAHCON ta ce, za ta rufe karbar kudin maniyyata, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta tabbatar a wata sanarwa.

Bincike daga Arewaci zuwa Kudancin kasar ya tabbatar da cewa, kalilan na maniyyata ne suka shirya biyan karin kudin da aka musu, yayin da da dama daga cikinsu suka hau kujerar naki, tare da neman hukumomin jin dadin alhazan jihohinsu su mayar musu da kudadensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.