Isa ga babban shafi

Matsalar tsaro za ta ta'azzara a Najeriya da makotanta - Behanzin

Tshohon Kwamishinan Harkokin Siyasa, tsaro da Zaman Lafiya na Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS Francis Behanzin ya yi gargadin yiwuwar sake tabarbarewar matsalolin tsaro a Najeriya da kasashen yankin Sahel.

Wasu mayaka a yankin Sahel
Wasu mayaka a yankin Sahel © SOULEYMANE AG ANARA / AFP
Talla

A wata zantawarsa da manema labarai a birnin Washington DC na Amurka dangane da tabarbarewar matsalolin tsaro a Najeriya da makwabtanta, Behanzin wanda kwararre ne a sha’anin tsaron Afrika, ya ce matsalolin na ci gaba da tabarbarewa a kowacce rana, wanda ke da nasaba da rashin hadin-kai a dukkanin fannonin yaki da matsala.

Behanzin wanda tsohon janar din soji ne ya ce duk da yadda kasashen na Najeriya da takwarorinta na Sahel ke ikirarin yaki da matsalolin tsaro, ba su da cikakkun tsare-tsaren da suka dace a bangaren soji da bangaren tafiyar da gwamnati. Kazalika babu manufofin tunkarar matsalar.

Hatta a makalar da ya gabatar a cibiyar tsaro da zaman lafiya da ke Amurka, Behanzin ya ce ana ci gaba da ganin ta’azzarar matsalolin tsaron a kusan dukkanin kasashen da ke tsakanin Senegal har zuwa Sudan duk kuwa da tsare-tsaren da aka gabatar ciki har da shigar Majalisar Dinkin Duniya da ya kai ga girke dakaru dubu 13 a Mali gabanin rushe su a farkon shekarar nan.

Masanin wanda ke ci gaba da alakanta matsalar tsaron Najeriya da makwabtanta kan abin da ya biyo bayan yakin Libya, duk da yunkurin kasashen Amurka da Faransa da kuma Kungiyar ECOWAS a baya na ganin an shawo kan matsalolin tsaron, rashin kulawa daga gwamnatocin kasashen da kuma juyin mulkin da wasu kasashe suka fuskanta zai sake ta’azzara matsalolin tsaron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.