Isa ga babban shafi

Najeriya za ta kwaso 'yan kasarta da ke gudun hijira a kasashen Kamaru da Chadi

Gwamnatin Najeriya ta ce, za ta kwaso ‘yan kasarta akalla 6000 da ke zaman gudun hijira a kasashen Kamaru da chadi.

Wasu 'yan gudun hijira da aka dauko daga Muna da ke birnin Maidugurin jihar Borono a arewa maso gabashin Najeriya
Wasu 'yan gudun hijira da aka dauko daga Muna da ke birnin Maidugurin jihar Borono a arewa maso gabashin Najeriya REUTERS/Paul Carsten
Talla

Kwamishina a hukumar kula da ‘yan gudun hijira da bakin haure, Tijjani Ahmed wanda ya bayyana hakan a Abuja, y ace akalla ‘yan Najeriya dubu 21 ke zaman gudun hijira a kasar Chadi, yayin da dubu 14 ke Kamaru da sauransu.

Ya kara da cewa, daga cikin wadannan adadi, za a kwaso mutum 6,000 daga Chadi, yayin da har yanzu ba a gama tantance adadin mutanen da za a kwaso a kasar Kamaru ba.

A cewar sa, nan da watanni biyu masu zuwa ake sa ran kammala wannan aiki, da ya ce suna kan tattaunawa da gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, game da inda za a ajiye da zarar an dawo da su gida.

Gwamnatin kasar ta ce, akwai shirin basu horo na musamman kan yadfda za su dogara da kan su amma karkashin kulawar gwamnatin jihar Borno, domin gwamnatin ba za ta iya daukar dawainiyarsu kai tsaye ba.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar, ta ce da dama daga cikin wadanda abin ya shafa, sun rasa matsugunansu ne sakamakon mummunar ambaliyar da ta auku a shekarar 2022, hare-haren mayakan Boko Harama da kuma rikicin manoma da makiyaya, sai kuma sauyin yanayi da ya addabi yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

Kwaminsinan hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Bernadette Muteshi, yay aba da wannan mataki da gwamnatin Najeriya ta bullo da shi, tare da fatan dorewar hakan da kuma tallafawa rayuwar ‘yan gudun hijirar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.