Isa ga babban shafi

Masu bincike sun daurawa Gwamnatin Africa ta kudu laifin tashin gobarar da ta kashe mutane 77

Binciken masana kan faruwar bala’o’i a Afrika ta Kudu ya dorawa gwamnatin kasar Alhakin tashin wata gobara da ta yi sanadin mutuwar mutane 77.

Gobarar ta kashe mutane sama da 77
Gobarar ta kashe mutane sama da 77 AFP
Talla

Binciken ya yi bayani filla-filla kan yadda mahukunta suka kawar da idanun su ga barin ganin yadda mutanen suka yiwa ginin yawa, yayin da suka chunkushe hanyar da jami’an kwana-kwana zasu wuce idan bukatar hakan ta taso.

Binciken ya kuma ci gaba da bayani kan yadda ya gano yadda mazauna dogon ginin na birnin Johannesburg suka mayar da shi maboyar muggan makamai, kisan kai ta’ammali da kuma safarar miyagun kwayoyi.

Binciken ya kuma zargi jami‘an hukumar kashe gobara da jan kafa kafin zuwa wajen da wutar ta tashin lamarin da ya yi sanadin karuwar wadanda suka rasa rayukan su.

A ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata ne wuutar ta tashi, wadda ta kone mutane kurmus ta yadda sai da aka rika amfani da gwajin kwayoyin hallita kafin gano ainahin mutanen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.