Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 7 na fama da matsananciyar yunwa a kasashen Sahel 3- Rahoto

Kungiyar agaji ta International Rescue Commitee IRC ta bayyana karuwar adadin mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa a kasashen Sahel 3 da ke karkashin mulkin Soji zuwa mutane miliyan 7 da rabi, lamarin da ke nuna tsananin bukatar agajin abincin da al’ummar kasashen na Burkina Faso da Mali da kuma Nijar ke ciki.

Rahoton na Majalisar ya bukaci samar da gyare-gyaren da zasu kai ga yakar matsalar ta yunwa wadda ta fi tsananta a kasashen Afrika da kuma yankunan da yaki ya daidaita.
Rahoton na Majalisar ya bukaci samar da gyare-gyaren da zasu kai ga yakar matsalar ta yunwa wadda ta fi tsananta a kasashen Afrika da kuma yankunan da yaki ya daidaita. REUTERS/David Lewis
Talla

Cikin wani rahoton gargadi da IRC ta fitar a jiya Litinin ta ce yawan mutanen da ke fama da matsananciyar yunwar ya karu matuka lura da yadda ake da alkaluman mutane miliyan 5 da dubu 400 masu fama da yunwar a bara cikin kasashen 3 na Nijar da Mali da Burkina Faso.

Kasashen 3 na tsakiyar Sahel masu yawan jama’a miliyan 70 da dukkaninsu ke fama da matsalolin ayyukan ta’addanci, kungiyar ta IRC ta ce matsalar cutuka masu alaka da rashin abinci mai gina jiki na ci gaba da ta’azzara tsakanin al’ummomin kasashen musamman 3 musamman tsakanin kananan yara.

A cewar IRC wannan matsala ta karancin abinci ka iya watsuwa zuwa kasashen Kamaru da Chadi da kuma Najeriya tsakanin watan Yuni zuwa Agustan shekarar nan, wanda ken una bukatar daukar matakan gaggawa don wadata yankin na Sahel da abinci.

Sanarwar ta ruwaito mataimakin shugaban kungiyar na shiyyar yammacin Afrika Modou Diaw na cewa tun shekaru 5 da suka gabata, yankin yammaci da tsakiyar Afrika ke ganin barazanar karancin abincin, sai dai a bana matsalar ta ta’azzara fiye da hasashe.

Matsaloli masu alaka da sauyin yanayi sun haddasa karancin abinci yayinda matsalar tsaro ta tilasta al’ummomi da dama barin matsugunansu a kasashen 3 lamarin da ya kassara tsarin noma da samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.