Isa ga babban shafi

Kotu a Ivory coast ta daure wasu mutane 13 a gidan yari saboda safarar hodar iblis

Kotu a birnin Abidjan na Ivory Coast ta yanke wa wasu mutane 13 hukunci daurin shekaru 10 a gidan yari ciki kuwa har da wani dan asalin kasar Spaniya, a sakamakon kama su da hannu a safarar hodar iblis tsakanin kasashen duniya.

Yawan hodar iblis din da aka kama ya kai tan biyu
Yawan hodar iblis din da aka kama ya kai tan biyu ASSOCIATED PRESS - NATHAN DENETTE
Talla

A watan Afrilu 2022 ne dai aka kama mutanen da hodar iblis da nauyin ta ya kai tan biyu a birnin San Pedro da ke gabar ruwan kasar.

Bayanai sun ce kiyasin hodar iblis din zai kai CFA biliyan 41, kwatankwacin yuro miliyan 62, kuma ba tare da bata lokaci ba aka kama mutane sama da 30 da ke da alaka da laifin.

Cikin wadanda aka kama har da wasu manyan yan kasuwa 3 wadanda su kuma aka yanke musu hukuncin watanni 24 da kuma tarar CFA miliyan 30 kowannen su.

Bincike ya nuna cewa akwai manyan masu wannan harkalla da ke daukar nauyin safarar hodar iblis cikin kasar daga kasashen Kudancin Amurka, wasu kasashen Nahiyar Afrika da kuma Turai.

Ko da yake mayar da martani bayan yanke hukuncin, babban mai gabatar da kara kuma lauyan gwamnati Me Abdoulaye Ben Méité, ya yaba da hukuncin, yana mai cewa ba makawa zai zama izna ga masu shirin aikata irin wannan laifi a gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.