Manyan jam'iyyun adawar Togo sun ce za su tirjewa sabon ƙundin tsarin mulki
Manyan jam'iyyun adawa a Togo sun bayyana shirin turjewa tare da tsayin daka wajen daukar matakai masu tsauri kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da ya sharewa shugaban kasar hanya.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Yayin wani taron manema labarai da suka shirya a hedkwatar jam'iyyar PT dake Lomé, babban birnin kasar sun ce tsugune bai kare ba kan wannan batu.
Sanarwar bayan taron ta ce duk da gagarumar zanga-zangar da al'umma masamman kungiyoyin farar hula da 'yan adawa suka yi, shugabannin kasar sun ci gaba da fifita bukatunsu maimakon na al'umma.
Sabon ƙundin tsarin mulki
A ranar 6 ga watan Mayu, shugaban kasar Faure Gnassingbe ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin da 'yan majalisar suka amince da shi a karatu na biyu a ranar 19 ga Afrilu, wanda ke tabbatar da cewa zai ci gaba da mulki bayan gagarumin nasarar da jam'iyyarsa ta Union for the Republic ta samu a zabukan 'yan majalisa da na yanki da ya gudana ranar 29 ga watan Afrilu.
A karkashin wannan gyara na kundin tsarin mulkin kasar, yanzu yan majalisu ne zasu zabi shugaban kasa maimakon zaben gama-gari daga al'umma.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu