Isa ga babban shafi

Ruto ya ba da hutun kwana guda don makokin wadanda ambaliya ta kashe a Kenya

Shugaba William Ruto na Kenya ya bayar da hutu daga Juma’a ga daukacin al’ummar kasar don makokin mutane 238 da suka mutu a mummunar ambaliyar ruwan da kasar ke fama da shi yanzu haka.

Wani yanki da ambaliya ta tsananta a Kenya.
Wani yanki da ambaliya ta tsananta a Kenya. AP - Patrick Ngugi
Talla

A jawabinsa na ranar Laraba, Ruto ya ce za a yi amfani da ranar ta gobe juma’a wajen dasa tarin bishiyoyi don rage illar da dumamar yanayi ke yi wa kasar.

Kenya da sauran kasashen makwabtanta na gabashin Afrika na ganin ambaliyar ruwa mai munin gaske a damunar bana, inda zuwa yanzu iyalai fiye da dubu 235 suka rasa matsugunansu lamarin da ya kai ga kafa gomman tantunan wucin gadi ga jama’a don basu mafaka.

Shugaba Ruto ya kuma sanar da shirin bude makarantu a makon gobe, bayan dakatarwar akalla makwanni biyu sakamakon tsanantar ambaliyar wadda ta shafi makarantu fiye da dubu guda a sassan kasar.

Tuni dai shugaban ya yi umarnin gaggauta fara aikin gyaran makarantun da ambaliyar ta lalata.

Sai dai hukumar kula da yanayi ta Kenya ta ce kasar za ta ci gaba da ganin zubar ruwan sama ba kakautawa duk da cewa dai bazai yi yawan wanda kasar ta gani a baya ba.

Gwamnatin Kenya dai ta kwashe ilahirin mutanen da ke yankuna masu hadari musamman wadanda ke dab da tafkuna ko rafi ko kuma kogi don basu kariya daga hadarin ambaliyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.