Isa ga babban shafi

Biden ya bukaci hadin kan Majalisa don ci gaba da farfado da tattalin arziki

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira da a samu hadin kan kasa, inda ya wasa gwamnatinsa kan nasarar da ta samu na farfado da tattalin arzikin kasar bayan mawuyacin halin da ya shiga. 

Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi gaban majalisar dokokin kasar. 08/02/2023
Shugaban Amurka Joe Biden yayin jawabi gaban majalisar dokokin kasar. 08/02/2023 via REUTERS - POOL
Talla

Shugaban ya yi kiran ne, a lokacin da yake gabatar da jawabi kan halin da Amurka ke ciki a gaban taron majalisar dokokin kasar. 

Biden yace “Tarihin Amurka na cike da samun cigaba da juriya, koda yaushe cigaba muke samu ba tare da gazawa ba, mu ne kadai kasar da a duk lokkacin da muka shiga cikin matsala muke fita da karfi fiye da yadda muka fuakanci kalubalen”. 

Shugaba ya kara da cewa abinda suka sake maimaitawa kenan, shekaru biyu bayan tattalin arzikin kasar yayi rauni, saboda annobar korana da wasu matsaloli amma a yanzu da taimakon akasarin ‘yan kasar ya samu nasarar samar da karin guraben ayyukan yi har miliyan 12, adadin da ya zarce na duk wani shugaban kasa da ya samar a cikin shekaru 4. 

Yayin da yake fuskantar ‘yan Republican da ke da rinjayi a majalisar wakilai, Biden ya ambato wasu dokoki da suka samu amincewar ‘yan majalisar Republican da Democrat da suka hada da gagarumin kudurin gine-gine, da taimakon Ukraine da kuma kudurin kare ‘yancin auren jinsi daya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.