Isa ga babban shafi

Amurka ta yi barazanar haramta TikTok kan alakar shugaban manhajar da China

Shugaban manhajar TikTok, Shou Zi Chew ya bayyana a gaban ‘yan majalisar dokokin Amurka da suka yi masa zafafen tambayoyi bisa zargin cewa, akwai alaka tsakanin manhajarsa da China, baya ga hatsarin da suka ce ta na da shi ga matasa. 

Manhajar TikTok na ci gaba da samun karbuwa a sassan Duniya inda matasa fiye da miliyan 150 ke amfani da ita a Amurka.
Manhajar TikTok na ci gaba da samun karbuwa a sassan Duniya inda matasa fiye da miliyan 150 ke amfani da ita a Amurka. AP - Damian Dovarganes
Talla

Mr. Chew mai shekaru 40 dan asalin Singapore ya sha wuya wajen amsa tambayoyin da ‘yan majalisar Amurka daga bangaren Republican da Democrat suka yi masa bayan sun yi fargabar cewa, gwamnatin China za ta iya fakewa karkashin wannan manhaja ta TikTok wajen gudanar da leken asiri da tattara bayannan sirri har ma da kare manufofin Jam’iyyar Kwamunisancin kasar. 

Shugaban na Tiktok wanda ya kammala karatunsa a jami’ar Havard kuma tsohon ma’aikacin banki, ya gaza warware zargin barazanarda aka ce tiktok na yi wa Amurka bayan kwashe tsawon sa’o’i ya na shan tambayoyin. 

Shugaban Manhajar TikTok Shou Zi Chew yayin jawabi gaban Majalisar dokokin Amurka.
Shugaban Manhajar TikTok Shou Zi Chew yayin jawabi gaban Majalisar dokokin Amurka. AP - Jacquelyn Martin

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da manhajar ke fafutukar tsallake wa’adin da fadar White House ta ba ta kan cewa, ko dai ta yanke alaka da China ko kuma a haramta amfani da ita a fadin Amurka. 

Shi dai Mista Chew a yayin amsa tambayoyin, ya ce, babu abin da ya hada manhajar ta tiktok da gwamnatin China. 

Muddin gwamnatin Amurka ta haramta amfani da tiktok a fadin kasar, hakan zai hana akalla mutane miliyan 150 akasarinsu matasa, samun nishadin da suka saba da shi a fadin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.