Isa ga babban shafi

Amurka za ta tura karin jiragen ruwa yankin Gulf saboda Iran

Amurka na shirin aike da karin jiragen ruwan yaki da dubban sojojin ruwa zuwa yankin Gabas ta Tsakiya domin kara tabbatar da tsaron teku, sakamakon yunkurin Iran na kwace jiragen ruwan kasuwanci a can.

Amurka ta ce matakin martani ne ga kasar Iran.
Amurka ta ce matakin martani ne ga kasar Iran. AP
Talla

Hukumomin kasar ta Amurka sun ce, Sakataren tsaro Lloyd Austin ya amince da tura rundunar fafutuka ta USS Bataan da kuma runduna ta 26 ta jiragen ruwa zuwa yankin Gulf.

Tawagar dai ta kunshi jiragen ruwa guda uku, ciki har da Bataan, wani jirgin ruwan dakon kaya, dauke da sojojin ruwa kusan 2,500.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Babban Rundunar tsaron Amurka ta ce tura sojojin zai samar da mafi girma da sassauci da karfin tsaron ruwa a yankin.

Sanarwar ba ta ambaci sunayen jiragen ba, amma jami'an Amurka sun yi cikakken bayani kan sassan da ke da hannu wajen tura sojojin bisa sharadin sakaya sunansu don sanya idanu sosai kan shige-da-ficen sojojin.

Har ila yau, an shafe makwanni da dama ana kai harin da jirgin A-10 a can domin mayar da martani ga ayyukan Iran.

Iran ta yi kokarin kame wasu tankokin mai guda biyu a kusa da mashigin Hormuz a farkon wannan watan, inda suka bude wuta kan daya daga cikinsu.

Jirgin na yakin na da nufin ba da kariya ga jiragen ruwa na kasuwanci da ke ratsawa a matsayin gargadi ga Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.