Isa ga babban shafi

Trump ya ki amsa laifukan da ake tuhumarsa a gaban kotu

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi na kin amincewa da shan kaye da ikirarin nasara a zaben 2020, da kuma tinzira Amurkawa. 

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake gurfana a gaban kotu. 04/08/23
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake gurfana a gaban kotu. 04/08/23 AP - Alex Brandon
Talla

Trump, wanda ke sahun gaba a jerin ‘yan takara a zaben fidda gwani na jam'iyyar Republican a zabe shekarar 2024, ya yi watsi da zargin ne yayin wani dan takaitaccen sauraren kara da aka yi a kotun dake Washington DC, da aka yanke wa daruruwan magoya bayansa hukunci kan rawar da suka taka a harin da aka kai majalisar dokoki ta Capitol a ranar 6 ga Janairun 2021.

'Ban aikata wani laifi ba’, inji Trump bayan da mai shari'a Moxila Upadhyaya ta karanta tuhume-tuhumen da ake masa da kuma da kuma tanadin hukunci muddun aka same da aikata kaifi.

Lauya na musamman Jack Smith ya gabatar da tuhume-tuhumen cikin wani daftari mai shafuka 45.

Nasarar zaben 2020

Jim kadan kafin barin Bedminster, kulob dinsa na kwallon labu dake New Jersey domin kama hanya da girjin samansa zuwa babban birnin ƙasar, Trump jadda da iƙirarinsa mara tushe na cewa sace nasarar da ya samu a zaɓen na watan Nuwamba 2020 da ya sha kaye a hannun Joe Biden "an sace."

Tuni dai aka tuhumi attajirin mai shekaru 77 kan wasu laifuka biyu, da kuma wannan sabbin, daidai lokacin da ake shirye-shiryen fara yakin neman zaben na shekara mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.