Isa ga babban shafi

Koriya ta Arewa ta ce cin zarafi ne ya tilasta wa sojan Amurka shiga kasarta

Koriya ta Arewa ta ce, sojan Amurka Travis King ya tsallaka cikin kasarta a watan da ya gabata saboda cin zarafi da nuna wariyar launin fata da sojoji ke yi, yayin da kasar ta Amurka ke neman taimakon Majalisar Dinkin Duniya domin shiga tsakani wajen karbo sojan nata.

Majigi dauke da hoton sojan na Amurka Travis King da aka nuna a filin jirgin kasan Seoul.
Majigi dauke da hoton sojan na Amurka Travis King da aka nuna a filin jirgin kasan Seoul. AP - Ahn Young-joon
Talla

Matashin sojan mai shekaru 23 ya yi hatsari a kan iyaka daga Koriya ta Kudu a ranar 18 ga Yuli yayin da ya ke yawon shakatawa.

King ya amince cewa ya tsallaka kan iyaka ba bisa ka’ida ba kuma yana neman mafaka a kasar, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na KCNA ya rawaito.

Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin Pyongyang ta amince da tsare sojan.

Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar wadda ya zuwa yanzu kafafen yada labarai na cikin gida ne kawai suka wallafa, ba ta yi karin bayani kan lafiyar sojan na Amurka ba ko kuma za ta ba shi mafaka a matsayin dan gudun hijira ba.

Ana kara nuna damuwa game da halin da sojan na Amurka ke ciki, wanda ba a ji duriyarsa ba.

Amurka na kokarin zaman tattaunawa kan yadda za a sako sojan nata amma tare da taimakon rundunar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da yankin kan iyaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.