Isa ga babban shafi

Dan bindiga ya kashe bakaken fata 3 a jihar Florida ta Amurka

Akalla mutane 3 suka mutu yayin wani harin wariyar jinsi da ya faru a jihar Floridar Amurka, bayan da wani dan bindiga ya bude wuta kan masu hada-hada a wani shagon cinakayya ranar asabar din da ta gabata.

Hare-haren bindiga ba sabon abu ba ne a Amurka.
Hare-haren bindiga ba sabon abu ba ne a Amurka. AFP - -
Talla

Rundunar ‘yan sandan jihar Florida ta tabbatarwa manema labarai cewa dan bindigar farar fata ya zo ne kofar shagon cinakayyar cikin motarsa ya kuma bude wuta kan bakaken fatar da ke cinikayya a shagon mai rahusa inda nan ta ke mutum 3 suka mutu, kafin daga bisani ya kasha kansa da kansa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa, maharin wanda ya ke tsakanin shekaru 20 da ‘yan kai, shaidun gani da ido sun ji shi ya na fadin cewa ya zo ne don ya yi kisa kuma kai tsaye ya tunkarai inda bakake suke ya yi musu dauki dai-dai.

A cewar shaidun maharin na dauke da bindiga kirar AR rataye a wuyansa da kuma wata karamar bindigar hannunsa lamarin da ya sanya jami’an tsaron  shagon cinikayyar na Dollar General store gaza tunkararsa.

Lamarin dai ya faru ne a gab da jami’ar Edward Waters University wato dadddiyar jami’ar bakaken fatar nan mai dogon tarihi da ke jihar ta Florida a kudancin Amurka.  

Wasu rahotanni na daban sun ce maharin ya kwana ne a dakunan dalibai na jami’ar sai dai babu rahoton ko ya cutar da wasu a ciki.

Babu dai cikkaken bayan ikan makashin ko kuma inda ya fito koma cikakken sunanshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.