Isa ga babban shafi

Amurka ta gargadi Korea ta Arewa kan shirin sayar wa Rasha makamai

Amurka ta gargadi Korea ta Arewa game da shirin sayar wa Rasha harsasai wadanda za ta yi amfani da su wajen ci gaba da yakin da ta ke a Ukraine.

Shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa yayin liyafar cin abinci da ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a ziyarar da ya kai Pyongyang cikin watan Yulin da ya gabata.
Shugaba Kim Jong Un na Korea ta Arewa yayin liyafar cin abinci da ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu a ziyarar da ya kai Pyongyang cikin watan Yulin da ya gabata. AP
Talla

Gargadin na Amurka da ke zuwa a daidai lokacin da takun-saka ke ci gaba da tsananta tsakanin kasar da Korea ta Arewan ta ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna yadda Moscow ta karkata ga Pyongyang don samun harsasan ci gaba da yaki.

Kakakin Ma’aikatar Tsaron Fadar White House John Kirby ya bayyana cewa Amurka ta damu matuka kuma tana sanya idanu kan tattaunawar cinikin makaman da ke gudana tsakanin Rasha da Korea ta Arewa.

Sanarwar ta ce, wajibi ne Korea ta Arewa ta yi biyayya ga dokokin da suka haramta mata sayar da kowanne irin makami ga Rasha.

A cewar sanarwar, Amurka na da masaniya kan yadda Ministan Tsaron Rasha Sergei Shoigu ke kokarin shawo kan Pyongyang don ganin ta sayarwa Moscow harsasan bindigogin atilari.

A watan Yulin da ya gabata ne Ministan Tsaron na Rasha ya kai ziyara Korea ta Arewa inda ya gana da shugaba Kim Jong Un kuma ana ganin yayin ganawarsu ne suka tattauna batun sayar da makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.