Isa ga babban shafi

Guguwar Idalia ta katse wa Amurkawa dubu 240 wutar lantarki

Sama da mazauna jihar Florida ta Amurka  dubu 240 ne suke cikin duhu skamakon katsewar wutar lantarki, biyo bayan ta’adin da mahaukaciyar guguwar Idalia ta yi a wasu yankuna, bayan da ta isa jihar a ranar Larabar nan. 

Dubban Amurka sun rasa wutar lantarki sakamakon guguwar Idalia.
Dubban Amurka sun rasa wutar lantarki sakamakon guguwar Idalia. AP - Rebecca Blackwell
Talla

Hukumar da ke bibiyar batun da ya shafi daukewar wutar lantarki a Amurka, wato PowerOutage ta ce mutane dubu 243 da 521 ne suka tsinci kansu a cikin rashin wutar lantarki tun daga tsakar ranar Laraba, kuma yankin Big Bend na jihar ne lamarin ya fi shafa, inda kananan hukumomin Taylor, Lafayette da Wakulla ke da kashi 65 na wannan matsala ta rashin wuta. 

Guguwar ta isa jihar ne da safiyar Laraba, a cewar Cibiyar Hasashen Yanayi da ke mayar da hankali a kan guguwa, kuma  a halin da ake ciki tana gudun mil 110 ne a cikin sa’a guda. 

Tun da farko a ranar Talata, sai da shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa a yankin, Deane Criswell ya gargadi al’ummar Florida kada su dauki batun wannan guguwar da wasa duk da cewa ba bakon abu ba ne a gare su. 

Guguwar  Idalia ce mahaukaciyar guguwa  ta 3 da jihar Florida ta fuskanta a cikin watanni 12, bayan guguwar Ian da ta isa jihar a watan Satumban bara, sai  kuma guguwar Nicole a watan Nuwamba. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.