Isa ga babban shafi

Rasha ta dana wani makami mai linzami cikin shirin ko ta kwana

Rasha ta yi Shirin ko ta kwana, game da yuwuwar amfani da wani makami mai linzami na zamani wanda shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce shiri ne game da barazanar da ake yiwa kasarsa.

Rasha ta yi gwajin harba makami mai linzami na Sarmat a watan Afrilun 2022 a yankin Plesetsk na kasar.
Rasha ta yi gwajin harba makami mai linzami na Sarmat a watan Afrilun 2022 a yankin Plesetsk na kasar. © AFP
Talla

Shugaban hukumar binciken sararin samaniya ta Rasha Yuri Borisov, ya ce an dana makami mai linzamin na Sarmat da sunan shiryawa abokan gaba.

Bisa bayanan masana, RS-28 Sarmat na iya isar da wani jirgin yaki na MIRVed mai nauyin ton 10 zuwa kowane wuri a duniya da za a aika shi.

Kakakin Majalisar Tsaron Fadar White House John Kirby ya bayyana a ranar Juma'a cewa ba shi da ikon tabbatar da rahotannin da ke cewa Rasha ta sanya Sarmat a cikin shirin ko ta kwana.

Wannan makami mai linzamin na Sarmat dai wani makami ne na karkashin kasa wanda jami'an Rasha suka ce yana iya daukar makaman kare dangi har guda 15.

Sarmat yana da nauyin fiye da ton 200, kuma yana da nisan kilomita 18,000 wanda aka kera don maye gurbin tsofaffin makamai masu linzami da aka kera a shekarun 1980.

Rasha ta yi gwajin harba makami mai linzami na Sarmat a watan Afrilun 2022 a yankin Plesetsk na kasar, wanda ke da nisan kilomita 800 daga arewacin Moscow, kuma makamin da aka harba ya sauka ne a Kamchatka, yankin gabas mai nisa a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.