Isa ga babban shafi

Amurka da kawayenta sun sha alwashin taimakawa Isra'ila wajen kare kanta

Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya da kuma Amurka sun fidda sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi Allah wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai Isra’ila, tare da yin alkawarin taimakawa kasar wajen kare kanta.

Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya da kuma Amurka sun yi Allah wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai Isra’ila.
Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Italiya da kuma Amurka sun yi Allah wadai da harin da kungiyar Hamas ta kai Isra’ila. AP - Andrew Harnik
Talla

Sanarwar dai ta biyo bayan ganawa ta waya tsakanin Firaministan Burtaniya Rishi Sunak da shugaban Amurka Joe Biden da Emmanuel Macron na Faransa da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da kuma Firaministar Italiya Giorgia Meloni suka yi.

Kasashen sun bayyana rashin din dadinsu kan harin da Hamas ta kai Isra’ila, wanda suka bayyana a matsayin na ta’addanci, musamman yadda suka ce kungiyar ta kashe mutanen da basuji basu gani ba tare da kame wasu da ta yi.

Shugabannin sun ce kasashensu za su marawa Isra'ila baya a kokarinta na kare kanta da al'ummarta daga irin wannan ta'asa na Hamas.

Tankokin yakin Isra'ila.
Tankokin yakin Isra'ila. AP - Ohad Zwigenberg

Sanarwar ta kara da cewa kasashe biyar sun amince da halalcin muradun al'ummar Falasdinawa, kuma suna goyon bayan daidaiton adalci na cin gashin kai tsakanin Isra'ila da Falasdinawa, sai dai sun ce ko kadan Hamas ba ta bayar da gudunmar da ta dace ga al'ummar Falasdinawa, face ta’addanci da zubar da jini da ta yi.

Shugabannin kasashen sun ce cikin kwanaki masu zuwa, za su ci gaba da haka kai a matsayinsu na aminan Isra'ila, don tabbatar da cewa ta iya kare kanta, da kuma shimfida sharuddan samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

A ranar Abasar din da ta gabata ne dai, kungiyar Hamas ta kaddamar da hare-hare kan Isra’ila wanda ya yi sanadiyar mutane sama da dari 9 daga bangaren Isra’ila tare da raunata wasu sama da dubu daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.