Baki 'yan kasashen waje da dama ne suka bace a Isra'ila
Kasashen duniya na ci gaba da gabatar da alkaluman mutanen su da aka kashe ko suka bata sakamakon harin da kungiyar Hamas ta kaddamar a Isra’ila a karshen mako, abinda ya haifar da kazamin yakin dake gudana yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Kasar Amurka ke sahun gaba na yawan ‘yan kasashen ketare da rikicin ya ritsa da su, inda tace an kashe mata mutane 22, yayin da aka yi garkuwa da su, wasu kuma suka bata, sai Thailand wadda tace an kashe mata mutane 21, yayin da aka yi garkuwa da 16.
Ga jerin kasashen da suka bayyana adadin mutanen su da rikicin ya ritsa da su.
Kasashe Mutuwa Bata
Amurka 22 -
Thailand 21 16
Faransa 12 17
Nepal 10 1
Argentina 7 15
Ukraine 7 7
Russia 4 6
Birtaniya 4 -
Canada 3 3
China 3 2
Brazil 2 1
Peru 2 3
Philippines 2 3
Chile 1 1
Australia 1 -
Austria 1 2
Azerbaijan 1 -
Camboadia 1 -
Ireland 1 -
Turkiya 1 1
Portugal 1 4
Spain 1 -
Italia - 3
Paraguay - 2
Sri Lanka - 2
Tanzania - 2
Jamus -
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu