Isa ga babban shafi

Kusan Falasdinawa dubu 10 ne suka mutu a Gaza

Kawo yanzu an tabbatar da mutuwar Falasdinawa dubu 9 da 770 da suka hada da kananan yara dubu 4 da 800 da suka riga mu gidan gaskiya a sanadiyar yakin da Isra'ila ke yi da mayakan Hamas a Zirin Gaza.

Wasu daga cikin Falasdinawa da yaki ya daidaita rayuwarsu  a Gaza
Wasu daga cikin Falasdinawa da yaki ya daidaita rayuwarsu a Gaza AFP - BASHAR TALEB
Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a kasashen duniya da dama don ganin a tsagaita bude wuta a Gaza.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa, ba za su cimma wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta ba har sai mayakan Hamas sun maido da Yahudawa 240 da suka yi garkuwa da su tun ranar 7 ga watan Oktoba, lokacin da suka kaddamar da harin da ya kashe mutane dubu 1 da 400 a Isra'ila.

Kasashen Larabawa sun yi wa Amurka matsin lamba kan tsagaita wuta

Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas ya bi sahun takwarorinsa na kasashen Larabawa da suka bukaci tsagaita bude wuta a Zirin Gaza a yayin ganawar da ya yi da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken a yau Lahadi.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken tare da shugaban Falasdinu ahmoud Abbas.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken tare da shugaban Falasdinu ahmoud Abbas. AFP - JONATHAN ERNST

A jiye na Masar da Jordan suka yi wa Blinken matsin lamba don ganin na tsagaita bude wuta a Gaza, amma Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya dage kan cewa, tsagaita bude wutar, ba koma za ta haifar ba illa bai wa mayakan Hamas damar sake kintsawa don kaddamar da farmaki kan Isra’ila.

 

Sai dai Blinken da ya kai wata ziyarar ba-zata a yankin Yammacin Kogin Jordan a wannan Lahadin, ya shaida wa  Abbas cewa, dole ne a kauce wa tursasa wa Falasdinawa ficewa daga muhallansu.

Ziyarar Blinken na zuwa ne ‘yan sa’o’i da wani jirgin yakin Isra’ila ya ragargaji sansanin ‘yan gudun hijira na Maghazi da ke tsakiyar birnin Gaza, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 45.

Isra'ila ta dakatar da ministan da ya bukaci jefa makamin nukiliya Gaza

Gwamnatin Isra’ila ta dakatar da wani ministan kasar saboda kiran da yayi na amfani da makamin nukiliya domin ragargaza yankin Gaza, a matsayin martani mai karfi a kan matakin da kungiyar Hamas ta dauka na kai mummunan hari a ranar 7 ga watan Oktoba.

Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu © Abir Sultan / AP

Ofishin Firaminista Benjamin Netanyahu ya sanar da dakatar da ministan mai suna Amichay Eliyahu wanda ya bukaci jefa bam din domin hallaka duk wani da ke yankin ciki har da Yahudawan da mayakan Hamas suka yi garkuwa da su.

Eliyahu wanda ya fito daga cikin kawance masu tsatsauran ra’ayin dake tare da Netanyahu, ya bayyana matsayin sa ne lokacin da yake amsa tambayoyi a wani gidan rediyo mai suna Kol Barama, lokacin da yace bai gamsu da irin matakan sojin da kasar ke dauka ba domin murkushe mayakan Hamas da suka kai hari kudancin Isra’ila wanda ya hallaka mutane dubu 1 da 400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.