Koriya ta Arewa ta harba tauraron dan adam na leken asiri sararin samaniya
Koriya ta Arewa ta ce ta yi nasarar harba wani tauraron dan adam na leken asiri na soji a sararin samaniya bayan rashin nasara har sau biyu a baya, yayin da Amurka ta jagoranci kawayenta wajen yin Allah wadai da matakin da cewa ya sabawa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.
Wallafawa ranar:
Wani kombo da ke dauke da tauraron dan adam da aka yi wa lakabi da Mallihyong -1 ya tashi cikin daren Talata daga lardin North Phyongan ta hanyar da aka tanada zuwa sararin samaniya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na gwamnati KCNA ya sanar.
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya halarci harba kumbon, kuma ya taya masana kimiya da fasaha da ke da hannu a wannan aiki murna.
Nan take Amurka ta jagoranci yin Allah wadai da kaddamar da shirin a matsayin "cin zarafi" na takunkumin Majalisar Dinkin Duniya, ta kuma ce hakan na iya dagula zaman lafiyar yankin.
Kamfanin dillancin labarai na Yonhap ya bayar da rahoton cewa, Koriya ta Kudu ta mayar da martani da cewa za ta koma aikin sa ido a kan iyakar kasar da Koriya ta Arewa da aka dakatar a shekarar 2018 a wani bangare na yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Seoul da Pyongyang na rage zaman dar-dar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu