Isa ga babban shafi

Wasu kasashe na kiraye-kirayen ganin an tsawaita yarjejeniyar Isra'ila da Hamas

Kasashen Masar da Qatar da kuma Amurka sun fara matsa kaimi wajen ganin an tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakanin Isra’ila da Hamas a wani yunkuri na ganin an kammala tseratar da ilahirin fursunonin da ke tsare, dai dai lokacin da aka shiga ranar karshe ta yarjejeniyar.

Kasashen Masar da Qatar da kuma Amurka ne kan gaba wajen kiraye-kirayen ganin an tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar.
Des Palestiniens évacués de la bande de Gaza montent à bord d'un avion à l'aéroport international El-Arish d'Égypte à destination d'Abou Dhabi, le 27 novembre 2023, dans le cadre d'une mission humanitaire organisée par les Émirats arabes unis. AFP - KARIM SAHIB
Talla

Dai dai lokacin da kiraye-kiraye ke ci gaba da tsananta game da bukatar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar, Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya gabatar da jawabin karfafa gwiwa ga dakarun yahudawan da ke yankin Gaza ya na mai cewa babu abin da zai dakatar da su a hare-haren da suke kaiwa kan larabawan Falasdinu.

A wani bayanin na daban, Netanyahu ya shaidawa Joe Biden na Amurka cewa zai iya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wutar da akalla kwana guda bayan sakin Yahudawa 13 da wasu ‘yan Thailand 3 baya ga wani Bayahude mai shaidar zama a Rasha guda.

Wasu Fursunonin Falasdinu da Isra'ila ta saki.
Wasu Fursunonin Falasdinu da Isra'ila ta saki. REUTERS - AMMAR AWAD

Daga juma’ar da ta gabata kawo yanzu, Hamas ta karbi fiye da Falasdinawa 100 da Isra’ila ta kame wanda ke matsayin madadin fursunonin da ta saki, ciki kuwa har da wasu matasa 39 da ke tsare a gidan yari.

Tuni dai hankula suka karkata game da yiwuwar ko bangarorin biyu za su amince da ci gaba da tsagaita wutar ko akasin haka, dai dai lokacin da yarjejeniyar ke shirin kawo karshe da sanyin safiyar gobe Talata, wanda ke nuna bangarorin biyu za su ci gaba da yakin da suka faro tun ranar 7 ga watan jiya.

Duk da wannan yarjejeniya, dakarun Isra’ila da ke cikin yankin Gaza sun ci gaba da kai hare-hare tare da sumame a sassan daban-daban na zirin, yayinda su ke ci gaba da kame tarin mutane galibi kananan yara baya ga kisan daruruwa da kuma jikkata dubbai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.