Isa ga babban shafi

Kurdawa sun maka kamfanin Lafarge a kotu kan zargin ta'addanci

Daruruwan Amurkawa ‘yan Kurdawan Yazidi, a karkashin jagorancin macen nan da ta taba lashen kyautar zaman lafiya ta Nobel, Nadia Murad sun maka kamfanin simintin kasar Faransa Lafarge kotu, suna zargin sa da taimaka wa kungiyar  IS da kayan yaki a ta’asar da ta aikataa a Iraqi da Syria.

Kamfanin siminti na Lafarge
Kamfanin siminti na Lafarge © AFP/Franck Fife
Talla

‘Yan Yazidin, wadanda suka samu wakilicin wani lauyar kare hakkin dan adam, Amal Clooney  da wani tsohon jami’in diflomasiyya, Lee Wolosky, Amurkawa ne, wadanda ‘yan uwansu suka tsallake  rijiya da baya a rikicin na IS, wanda ya barke a arewacin Iraqi a shekarar 2014.

A cikin takardar karar da aka kai babban kotun birnin New York, ‘yan Yazidin sun zargi kamfanin Lafarge da taimaka wa IS wajen aikata abin da suka kira ayyukan ta’addanci na kasa da kasa.

‘Yan Yazidi dai wasu tsiraru ne mabiya  wani daddaden addini, wanda ya cakuda wani sashe na addinin Kiristancci, Musulinci da Yahudanci, kuma kungiyar Islamic States, wato IS ke daukar su a matsayin masu bautar shaidan.

A watan Oktoban shekarar da ta gabata kamfanin Larfarge ya amsa tuhumar da aka yi masa, amma ya ce ya biya wasu makudan kudade ga wasu kamfanonin da ake wa tambarin ta’addanci ciki har da ISIS, amma ya yi hakan ne don samun damar ci gaba da gudanar da ayyukansa a Syria.

Sakamakon haka ne Lafarge din ya amince ya biya diyyar dala miliyan dari 7 da 78.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.