Isa ga babban shafi

Amurka za ta bude iyakokinta da Mexico a wannan Alhamis

A wannan Alhamis ne Amurka za ta bude wasu kan iyakokinta hudu da Mexico a daidai lokacin da aka samu raguwar masu tsallakawa cikin kasar ta barauniyar hanya.

Amurka ta ce za ta muhimmanta batun samar da tsaro a kan iyakokinta da Mexico
Amurka ta ce za ta muhimmanta batun samar da tsaro a kan iyakokinta da Mexico AFP/File
Talla

Amurka za ta ci gaba da gudanar da ayyukan shige da fice a kan wata gadar kasa da kasa da ke Eagle Pass a Texas, sai kuma wasu iyakoki biyu da ke Arizona da kuma wata iyakar a kusa da San Diego a California kamar yadda jami’an kwastam da na tsaron iyakokin kasar suka bayyana.

Jami’an sun ce, za su ci gaba da bai wa batun samar da tsaro a kan iyakokin muhimmanci.

A cikin watan Disamba ne, hukumomin tsaron iyakokin Amurka suka yi kokarin tantance bakin haure a daidai lokacin da adadin wadanda aka tsare ya kai kusan mutun dubu 11 a cikin kwana guda, alkaluman da su ne mafi yawa da aka tattara a kasar.

Yanzu haka ‘yan majalisar dokokin kasar na gudanar da tattaunawa game da yiwuwar cimma wata yarjejeniya da za ta kunshi samar da matakan tsaron kan iyakoki.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce, ya kamata ‘yan majalisar su amince masa ya yi amfani da kudin da yake bukata domin samar da tsaro a kan iyaka.

Da ma a makon jiya ne, hukumomin Amurka da na Mexico suka lashi takobin yin aiki kafada da kafada domin tunkarar matsalar shige da fice a kan iyakokinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.