Isa ga babban shafi

Kasashe 5 sun goyi bayan karar Afrika ta kudu kan kisan kiyashin Isra'ila a Gaza

A gobe Alhamis ne kotun duniya ke shirin fara sauraron karar da Afrika ta kudu ta shigar gabanta kan zargin Isra’ila da aikata kisan kare dangi a Gaza, dai dai lokacin da kasar ta kudancin Afrika ke samun goyon bayan akalla kasashe 5 kan wannan kara.

Wani yanki da hare-haren Isra'ila ya lalata a Gaza.
Wani yanki da hare-haren Isra'ila ya lalata a Gaza. AP - Fatima Shbair
Talla

Zuwa yanzu kasashe 5 ciki har da Jordan da Turkiya da Malaysia baya ga kungiyar kasashe musulmi ta OIC sun goyi bayan wannan kara wanda tuni Amurka ta kalubalance shi.

A bangaren Isra’ila har yanzu Amurka kadai ke nuna goyon bayan na kai tsaye ga kisan kiyashin da kasar ke aikatawa larabawan yankin Gaza.

A karshen watan Disamban bara ne, Afrika ta kudu ta maka Isra’ila gaban kotun duniya bisa zarginta da kisan kiyashi a Gaza, matakin da kasashe da dama suka yi maraba da shi, duk da cewa dai kasar ta gaza samun goyon baya na kai tsaye.

Zuwa yanzu Isra’ila ta kasha Falasdinawan da yawansu ya haura dubu 23 adadin da kusan rabinsa ke wakiltar kananan yara.

Zaman shari’ar na gobe Alhamis zai zo a wani yanayi da kasashe suka mayar da hankali wajen ganin an tsagaita wuta a hare-haren Isra’ilan wanda zuwa yanzu ya rushe fiye da kashi 80 cikin dari na yankin Gaza.

Har zuwa yanzu dai galibin kasashe ciki har da na musulmi sun gaza goyon bayan karar ta Afrika ta kudu ta yadda suke bayanan da basa tabbatar da matsayarsu kan goyon baya ko akasin haka game da karar, inbanda Amurka da kai tsaye ta kalubalanci karar.

A bangare guda Isra’ilan ta bukaci Afrika ta kudu ta nazarci karar tare da musanta aikata kisan kare dangi a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.