Akwai sauran wadanda suka tsira daga kisan kare dangin yahudawa sama da dubu 254 a duniya-Bincike
Wani rahoton bincike ya nuna cewa akwai sauran mutane da suka tsira daga kisan kare dangi da Hitla na Jamus ya yiwa yahudawa da yawan su ya kai 245 a doron kasa.
Wallafawa ranar:
Kungiyar Claims Conference mai tattara irin barnar da wannan yaki ya haifar da kuma nemawa wadanda abin ya shafa hakkokin su ta ce cikin wannan adadi guda 119,300 na zaune a cikin Isra’ila yayin da guda 38,400 ke rayuwa a Amurka sai kuma guda 21,900 a Faransa da kuma guda 14,200 da ke zaune yanzu haka a Jamus.
Bayanai sun ce kusan dukannin wadannan mutane, na kananan yara lokacin da wannan rikici ya faru, kuma sun rayu ne a tsakanin sansanonin gudun Hijira da kuma hijira daga kasa zuwa kasa lokacin da suke yunkurin buya da kuma boye asalin su.
Tun bayan samar da kungiyar a shekarar 1951 ta yi nasarar karbar diyya daga Jamus da yawan ta ya kai dala biliyan 90, bayan yarjejeniyoyi daban-daban da aka rika kullawa.
Kungiyar ta ce cikin mutanen akwai wadanda ke fama da tabin kwakwalwa da sauran cututtuka da suka shafi bangarorin jiki wadanda suka samu a sakamakon tashin hankalin da suka gamu da shi lokacin yakin.
Wannan a iya cewa shine kammalallen rahoto na adadin mutanen da suka tsira daga wancan tashin hankali kuma suke a raye har yanzu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu