Isa ga babban shafi

Karar Isra'ila a ICC ba za ta shafi alakarmu da Afirka ta Kudu ba - Blinken

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce karar da Afirka ta Kudu shigar da Isra’ila gaban kotun Duniya kan tuhumarta da kisan kare dangi a Gaza, ba za ta raunana dangantakar da ke tsakaninsu ba, sai dai Blinkken din ya sake yin watsi da zargin aikata kisan kiyashin.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken. © Service de presse de la présidence ivoirienne
Talla

A ranar Juma’a ake sa ran Kotun Duniyar za ta yanke hukunci kan amincewa ko yin watsi da shaidun da Afirka ta Kudu ta gabatar mata kan tuhumar da take yi wa Isra’ila. Yayin tsokaci kan batun, Blinken ya ce Amurka na daukar Afirka ta Kudu da muhimmanci.

"Kamar yadda aka sani, muna nan kan bakanmu akan wannan shari’a, amma duk da haka ba shakka alakarmu da Afirka ta Kudu na da muhimmanci, alaka ce mai zurfi da kuma fadi, wadda ta hada fannoni da dama, dan haka samun sabani akan wani batu ba zai rusa kyakkkyawar huldar mu ba, akan lamurra daban daban."

A ranar Alhamis ne dai sakataren harkokin wajen na Amurka ya isa kasar Angola, inda daga nan ya karkare  ziyarar mako guda da ya kawo Afirka, domin karfafa dangantaka tsakanin kasashen nahiyar masu bin tsarin dimokaradiya da Amurka.

Daga cikin muhimman batutuwan da Blinken ya tattauna da shugaba Joao Lourenco akwai bunkasa noma a kasar mai arzikin man fetur da ma sauran sassan yammacin Afirka, inda sakataren harkokin wajen Amurkan ya ce akwai bukatar taimaka wa manoma wajen inganta irin amfanin gonar da suke nomawa, ta yadda nau’ikan irin za su rika jure matsalolin da Sauyin Yanayi ke haifar wa, ci gaban da ya ce baya ga ciyar da kanta, nahiyar Afirka za ta ba da gudunmawar wadatar abinci a fadin duniya.

Ziyarar Blinken wadda ta kai shi ga kasashen Ivory Coast da Cape Verde da kuma Najeriya, ta zo ne a daidai lokacin da akasarin ‘yan Afirka ke kokawa akan yadda Amurka ke bai wa Isra’ila tallafin biliyoyin dala a yayin da take ci gaba ragargaza Zirin Gaza da sunan yaki da Hamas, sai kuma taimakon makudan kudaden da ta ke bai wa Ukraine a yakinta da Rasha.

Tuni dai kasar China da ke zaman babar abokiyar hamayyar Amurka ta fadada tasirinta a nahiyar Afirka ta hanyar zuba makudan kuddade wajen gudanar da manyan ayyuka, yayin da Rasha da suke yakin cacar baka, ta kulla yarjejeniyar soji da baki dayan kasashen Afirkan da sojoji suka yi juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.