Isa ga babban shafi
UKRAINE

Kungiyar Tarayyar Turai ta sake laftawa Rasha takunkumai

Kungiyar Tarayyar Turai ta sake lafta wani kunshin takunkumai 13 kan Rasha game da yakin da ta ke a Ukraine, takunkuman da zai shafi kamfanoni da kasuwanci da kuma daidaikun mutane akalla 200 da ke taimakawa Moscow da makamai a yakin na Kiev tare da garkuwa da kananan yara.

SHugaban Rasha, Vladimir Putin yayin wani taron manema labarai a birnin Moscow, ranar 19 ga Disamba, 2019.
SHugaban Rasha, Vladimir Putin yayin wani taron manema labarai a birnin Moscow, ranar 19 ga Disamba, 2019. AP - Pavel Golovkin
Talla

Belgium da ke jagoranci karba-karba na EU ta wallafa batun amincewa da takunkuman a shafin kungiyar na X inda ta ce ilahirin jakadun kungiyar sun amince da sabbin takunkuman a wani yunkuri na sake matsin lamba ga Rasha.

Haka zalika, Firaministan Norway Jonas Gahr Store ya bayyana cewa ko kadan baya daga cikin manufofin Rasha shiga yaki da kowacce kasa da ke cikin kungiyar tsaro ta NATO sai dai duk da haka kasashen kungiyar na bukatar zage dantse a bangaren tsaronsu.

Yayin zantawarsa da France24, Store wanda kasar ta sa ke cikin kasashen da suka assasa kungiyar ta NATO ya ce a halin da ake ciki ya zama wajibi ga kasashen Scandanivia su kulla kawance da NATO don baiwa kansu tsaro lura da cewa suke cikin hadarin mamaya daga Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.