Isa ga babban shafi

Yunwa ta fara kashe jarirai a Gaza bayan kasa cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

Wakilai daga kasashen Egypt, Qatar, Amurka Isra’ila da kuma Hamas na cigaba da zaman kawo karshen yakin Isra’ila da Hamas a birnin Doha dake kasar Qatar.

Yankin Rafah ne kadai ya ragewa al'ummar Gaza da ke da sauki kai hare-hare
Yankin Rafah ne kadai ya ragewa al'ummar Gaza da ke da sauki kai hare-hare AFP - MOHAMMED ABED
Talla

Bayanai na cewa tuni yunwa ta fara kashe jarirai a yankin Gaza, la’akari da yadda iyayen su ke tserewa suna barín su a dakunan kula da jarirai na asibitocin da ke gab da daina aiki saboda karancin wutar lantarki.

A makon da ya gabata ne Isra’ilar ta fara sakin wasu mutane 100 da ta ke rike da su tare da wasu firsunoni ‘yan kasar Falasdinu da ke hannunta, yayin da a wani bangaren kasashen Qatar, da Egypt da kuma Amurka ke fafutukar ganin cewa an sulhunta bagarorin biyu.

Wannan sulhu da Amurka, da wasu kasashen Larabawa ke kokarin yi, ya ba wa al’ummar yankin kwarin gwiwar cewa, za’a iya gano bakin zaren kafin watan ramadana da ke shirin kamawa.

A wani gefen kuma akwai rahoton da ke cewa daruruwan Falasdinawa ne ke tserewa daga mahallan su dake arewaci zuwa kudancin Gaza, sakamakon hare-haren da Isra’ila ke kai musu, duk da yunkurin sulhuntawa da ake yi.

A halin yanzu dai tsoro ya mamaye zukatan al’ummar Faladinun bayan  da Isra’ila ta fitar da sanarwar cewa za ta fara kai farmaki a Rafah, guda daga cikin manyan biranen kasar mai dauke da kusan mutane miliyan daya da rabi, yayin da hakan ya sa mazauna yankin tserewa zuwa iyakar Egypt.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.