Isa ga babban shafi

Zelensku ya alwashin murkushe Rasha a yakinsu na fiye da shekaru 2

Shugaban Ukraine ya lashi takobin fattakar Rasha a yakin da suke gwabzawa a tsakanisu, shugaban ya bayyana haka ne a yayin da ake taron cika shekaru biyu da Rasha ta mamaye kasar.

shugaban Ukraine yayin wata ganawarsa da shugaban Amurka Joe Biden
shugaban Ukraine yayin wata ganawarsa da shugaban Amurka Joe Biden © Evan Vucci / АР
Talla

Shugaban na Ukraine Volodymyr Zelensky ya sha alwashin samun nasara akan Rasha a yayin da ake cika shekaru biyu da mamayar da tayi a kasarsa, duk da karancin makaman yaki da dakarun kasar ke fama dashi.

Zelensky ya bayyana hakane a filin jirgin saman kasar a yayin da yake tarbar bakin da suka sauka a kasar domin halartar taron cika shekaru 2 da kasar ke fafata fada da Rasha.

Shugaban yayi wannan hasashe ne a yayin da yake ganawa da firaministocin kasashen Canada da na Italiya da kuma shugabar hukumar kungiyar gamayyar turai Ursula Vonder Leyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.