Isa ga babban shafi

Makomar Biden a zabe mai zuwa na cikin garari saboda yakin Gaza

Da dama daga cikin 'ya'yan jam'iyyar Democrat mai mulki a Amurka sun fusata matuka saboda matsayar shugaban kasar a yakin Gaza, lamarin da ka iya haifar masa da cikas a zaben watan Nuwamba kamar yadda wani sakamakon bincike na Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya nuna

Shuagaban Amurka Joe Biden
Shuagaban Amurka Joe Biden REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN
Talla

Reuters ya zanta da gomman manyan mambobin jam'iyyar Democrat da suka hada da jami'an gudanar da yakin neman zaben jam'iyyar har ma da masu kada kuri'a da masu rajin kare hakkin bil'adama.

Jiga-jigan jam'iyyar ta Democrat sun bayyana cewa, fadar White House ta yi zaton rikicin da jam'iyyar ke fuskanta zai yi sauki  a daidai lokacin da Biden ya kaddamar da yakin neman zabensa domin kalubalantar Donald Trump wanda ake kyautata zaton shi ne zai tsaya wa jam'iyyar Republican takara.

A yayin da ya rage watanni tara a gudanar da zaben, rikicin da ya dabaibaye jam'iyyar Democrat na ci gaba da  ta'azzara, kama daga matsin lamba daga 'yan adawa da ke kiran tsagaita musayar wuta ta din-din-din a Gaza da kuma fusatar da gungun masu kada masa kuri'a ya yi wanda ya taimaka masa lashe zaben 2020.

Wannan gungun ya kunshi Amurkawa bakaken fata da Musulmai masu rajin kare hakkin bil'adama da suka taimaka masa samun nasara a jihar Michigan wadda ta zame masa tilas ya lashe ta a wancan lokaci.

Binciken Reuters ya nuna cewa, jam'iyyar Democrat ta samu rarrabuwar kawuna sakamakon yadda Biden ya fito karara ya nuna goyon bayansa ga Isra'ila tun daga harin ranar 7  ga watan Oktoba da Hamas ta fara kaddamarwa da ya yi sanadiyar mutuwar Yahudawa kimanin dubu 1 da 200.

Da dama daga cikin Yahudawan Amurka da suka kada kuri'a ga Democrat sun nuna adawa da matsayar Biden a yakin na Gaza, ganin irin dimbin rayukan mutanen da aka kashe da adadinsu ya doshi dubu 30.

Tuni Biden ya gana da Larabawa mazauna Amurka a Michigan bayan sun lashi takobin juya masa baya a zaben na watan Nuwamba, lamarin da ya kara jefa makomarsa ta yin tazarce cikin rudani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.