Isa ga babban shafi

Amurka za ta baiwa Falasdinawa karin tallafin Dala miliyan 53

Kasar Amurka ta sanar da karin tallafin dala miliyan 53 domin taimakawa Falasdinawa, yayin da shugabar hukumar dake kula da ci gaban kasashen ketare a kasar ta bukaci bai wa jami’an aikin agaji kariyar da suke bukata domin gudanar da ayyukan su a Gaza.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden REUTERS - LEAH MILLIS
Talla

Shugabar hukumar ta Amurka dake kula da harkokin kasashen ketare, Samanther Power tace za’a mika kudaden agajin ga Falasdinawan dake bukata ne ta hannun hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kan su dake aiki a Gaza, ganin yadda kasashen yammacin duniya suka ki amincewa da rawar da hukumar majalisar dinkin duniya ke takawa a yankin.

Power wadda ke magana a kasar Jordan, tace ya zama wajibi wannan taimako ya kai ga hannun Falasdinawan da suke bukatar sa.

Jami’ar ta ce ma’aikatan agajin dake aiki a Gaza na sadaukar da rayukan su wajen taimakawa mabukata samun abinda za su ci, saboda haka ya zama wajibi a basu kariyar da suke bukata, wajen kaucewa kai musu hari.

Wannan tallafi ya kawo adadin taimakon da Amurka ta bai wa Falasdinawa zuwa dala miliyan 180 tun bayan barkewar yakin Gaza, sakamakon harin ranar 7 ga watan Oktobar da ta gabata da kungiyar Hamas ta kai Israila.

A makwannin baya Amurka ta kai kayan agaji Masar ta jiragen saman yaki domin mikawa Falasdinawan dake Gaza, yayin da ita da kawayen ta na Turai suka katse tallafin da suke bai wa yankin ta hannun hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar dinkin duniya, saboda zargin wasu ma’aikatan tan a cewa suna da hannu wajen harin da Hamas ta kai wa Yahudawa.

Ganin yadda aka hana jami’an aikin jinkai na majalisar aiki a yankin, Majalisar dinkin duniya ta gabatar da gargadin samun yunwa a tsakanin mazauna Gazar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.