Isa ga babban shafi

Amurka ta mika wa Isra'ila bukatar tsagaita wutar makwanni 6 a Gaza

Mataimakiyar shugaban Amurka, Kamala Harris ta bukaci kungiyar Hamas ta amince da tayin tsagaita wuta na makwanni 6 nan take, kana a wani kira mai kama da umarni, ta nemi Isra’ila ta kara azama wajen ganin an isar da kayakin agaji cikin Gaza. 

Mataimakiyar shugabar Amurka Kamala Harris.
Mataimakiyar shugabar Amurka Kamala Harris. AP - Kamran Jebreili
Talla

Kalaman Haris na jiya Lahadi shi ke matsayin mafi karfi da wani babban jami’in Amurka ya taba yi tun da Isra’ila ta fara kai hare-hare Gaza, a dai dai lokacin da shugaba Joe Biden ke fuskantar matsin lamba a kan goyon bayan Isra’ila, a yayin da adadin fararen hular da ke mutuwa a Gaza ke karuwa. 

Harris ta ci gaba da matsin lamba ga Isra’ila, kana ta zayyano wasu hanyoyin da za a iya bi wajen shigar da karin kayakin agaji birnin Rafah mai cinkoson jama’a, inda dubban mutane ke fama da matsananciyar yunwa, sakamakon hare-haren da Isra’ila ta shafe watanni biyar tana kai wa yankin. 

Kamala  Haris, wadda ta bukaci Hamas ta karbi wannan tayin na tsagaita wuta har na tsawon makwanni shida, ta ce yarjejeniyar za ta kai ga sakin wadanda aka yi garkuwa da su. 

Mataimakiyar shugaban na Amurka ta kara da cewa wajibi ne Isra’ila ta sake bude kan iyakoki, kana ya zama dole ta jingine batun takaita shigar da kayakin agaji Gaza. 

A ranar Asabar, wani babban jami’in Amurka ya ce Isra’ila ta amince da bukatar tsagaita wuta na makwanni 6, da sharadin Hamas za ta saki mafi rauni daga cikin wadanda ta ke garkuwa da su a Gaza. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.