Isa ga babban shafi

Amurka ta cafke dan Sudan ta Kudu bisa zargin sa da damfarar kasar

Amurka na tuhumar wani dan gwagwarmayar kasar Sudan kan zargin sa da hada kai da wani mutum mai suna Utah Man don sayan makamai na miliyoyin daloli da nufin shiga da su Sudan ba bisa ka’ida ba.

Tuni dai aka fara tuhumar mutanen a gaban wata kotu da ke Arizona
Tuni dai aka fara tuhumar mutanen a gaban wata kotu da ke Arizona AFP - STRINGER
Talla

Bayanai sun ce akwai kwakwaran zargi da ke nuna cewa za’a yi amfani da wadannan makamai ne wajen kaddamar da juyin mulki a kasar.

Mutumin da aka bayyana sunan sa da Peter Biar Ajak ya shiga Amurka da taimakon mahukunta shekaru 4 da suka gabata, bayan da yayi ikirarin cewa shugaban Sudan ya bada umarnin yin garkuwa da shi kuma a kashe shi.

A wancan lokaci gwamnatin Amurka ta bashi takardar izinin shiga kasar cikin gaggawa shi da iyalansa guda 4.

Babban mai gabatar da karar da ta shafi laifukan ta’addanci a jihar Arizona ya ce an gurfanar da Mr Ajak da wani mutum mai suna Abraham Chol Keech mai shekaru 44 da kuma Utah Man kan zargin yunkurin kitsa juyin mulki, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma mallakar makudan kudaden da gwamnati bata san da suba.

Makaman da Mr Peter da abokan aikin sa suka siya sun hadar da bindigogi kirar AK-47 da gurneti da bindigogi marasa kara, da kuma makaman missile da kananun bidigogi da kuma miliyoyin alburusai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.