Isa ga babban shafi

Sama da bakin-haure dubu 8 ne suka mutu a hanyar Turai a shekarar 2023- MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane dubu 8 da dari 5 da 65 ne suka mutu a kan hanyarsu ta balaguro zuwa nahiyar Turai a shekarar 2023, abin da ya sa shekarar ta zama mafi muni da hadari tun da aka fara tara bayanai a kan mace-macen da ke aukuwa ta irin wannan balaguro shekaru 10 da suka wuce.

Wani jirgin bakin-haure a kusa da tsibirin Lampedusa na Italiya a shekarar 2023.
Wani jirgin bakin-haure a kusa da tsibirin Lampedusa na Italiya a shekarar 2023. AP - Cecilia Fabiano
Talla

Hukumar kula da kaurar baki ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a wata sanarwa cewa adadin na shekarar 2023 yana wakiltan kashi 20 idan aka kwatanta da na shekarar 2022, lamarin da ke nuni da bukatar daukar matakan gaggawa don dakile karin asarar rayuka.

Hukumar ta ce adadin shekarar da ta gabata ya wuce wanda aka taba samu a shekarar 2016, lokacin da aka samu asarar rayuka har dubu 8 da 84.

A cikin wannan shekarar da ake ciki, mutane dari 5 da 12 sun riga sun mutu a yayin irin wannan balaguro mai hadari.

Tekun Mediterranean, inda bakin-haure da dama suke bi a kokarinsu na tsallakawa Turai daga  arewacin nahiyar Afrika ya ci gaba da kasancewa hanya mafi hadari, inda akalla mutane dubu 3 da dar da 12 suka mutu ko kuma suka bace.

Wannan shine adadi mafi yawa na bakin- haure da suka mutu a wannan hanya tun bayan shekarar 2017.

A nahiyar Afrika, akasarin wadanda suka mutu sun gamu da ajalinsu ne a Hamadar Sahara, da kuma hanyar zuwa tsibiran Canary na kasar Spain.

Kusan fiye da rabin mace-macen bakin-haure a shekarar 2023 sun auku ne sakamakon kifewar kwale-kwale, kana kashi 9 sun auku sakamakon hadari da ababen hawa, kashi 7 kuma saboda rikici da cin zali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.