Isa ga babban shafi

'Yan majalisar Amurka na shirin dakatar da tiktok daga kasar

China ta gargadi Amurka game da dakatar da kafar sada zumunta ta Tik-tok, tana mai cewa wannan mataki ba zai yi komai ba sai cutar da ita kanta.

Kamfanin na tiktok na zama barazana ga tsaron Amurka a cewar mahukuntan kasar
Kamfanin na tiktok na zama barazana ga tsaron Amurka a cewar mahukuntan kasar Photothek via Getty Images - Thomas Trutschel
Talla

‘Yan majalisar Amurka zasu kada kuri’a a yau Laraba game da dakatar da kafar sada zumuntar ta Tiko-tok a fadin kasar, da nufin tilastawa kamfanin barranta kansa da China matukar yana sha’awar ci gaba da zama a Amurka.

Wannan dai yana nuna irin karfin da kafar Tik-tok din mallakin China ke da shi.

Tuni China ta bakin ministan harkokin wajen ta Wang Wenbin ta yi watsi da wannan shiri na Amurka, tana mai cewa babu abinda zai yi illa yiwa Amurkan da ‘ya’yanta illa.

Amurkan na zargin kamfanin na Tik-tok da zama barazana ga tsaronta da kuma yi mata kutse a rumbunan adana muhimman bayanai, duk da dai bata bayar da wata shaida game da hakan ba.

Wang ya ce wannan dabi’a ta Amurka ba zata kara mata komai a wannan lokaci ba illa nunawa duniya karara yadda take kokari wajen dankwafe duk wata kasa da ta zo da abinda duniya ke maraba da shi, inda bai ta bace ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.