Isa ga babban shafi

Kasashe 40 sun gabatarwa Majalisar Dinkin Duniya matsayarsu kan fasahar AI

Kasashen duniya da dama sun gabatarwa majalisar dinkin matsayar su kan fasahar AI mai aiki irin na dan Adam.

Kasashen duniya na cigaba da nuna fargaba a game da fara amfani gadan-gadan da fashar ta AI
Kasashen duniya na cigaba da nuna fargaba a game da fara amfani gadan-gadan da fashar ta AI AFP - KIRILL KUDRYAVTSEV
Talla

Wakiliyar majalisar dinkin duniya a Amurka Linda Thomas-Greenfiled ta ce bayanan da ke kunshe cikin kundin da kasashen suka gabatar sun bukaci yin duba na tsanaki game da rawar da AI din zai taka a fannin tattalin arziki da kuma zamantakewa.

Amurka na cikin kasashe 40 da suka gabatar da matsayar su kan fasahar ta AI, yayin da anata bangaren take bukatar fayyace irin cigaba da dan adam zai samu yayin amfani da wannan fasaha.

Uwargida Linda ta gabatar da jawabin a madadin kasashen Argentina, Australia, Austria, Bahamas, Belgium, Bulgaria, Cabo Verde, Canada, Chile, Côte d’Ivoire, Croatia, Cyprus, Czechia, Denmark, Djibouti, Dominican Republic, Estonia, tarayyar Turai, Finland, Faransa, Georgia, Jamus, Greece, Hungary, Iceland, India, Ireland, Israel, Italiya, Japan, Kenya, Latvia, Liberia, Lithuania, Luxembourg, Malta, Montenegro, Morocco, Netherlands, New Zealand, Peru, Poland, Portugal, Koriya, Romania, Singapore, Slovakia, Slovenia, Spaniya, Sweden, Turkiyya, Hadaddiyar daular larabawa, Burtaniya, da Uzbekistan.

Ana sa ran nan gaba karin wasu kasashen 139 zasu gabatar da tasu matsayar.

Majalisar zata yi duba kan wannan kundi ta kuma duba yiwuwar biyan bukatun da ke cikin sa ranar 21 ga watan da muke ciki na Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.