Isa ga babban shafi

Amurka ta ja baya wajen taimaka mana don kubutar da mutanenmu - Netanyahu

Firaministan Israel Benjamin Natenyahu ya dakatar da ziyarar da manyan jakadun kasar suka shirya kai wa Amurka, a wani bangare na nuna fushinsa kan yadda Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da bada umarnin tsagaita wuta a Gaza.

Firaministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya dakatar da ziyarar da manyan jakadun kasar suka shirya kaiwa Amurka a wani bangare na nuna fushin sa kan amince da bada umarnin tsagaita wuta a Gaza.
Firaministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya dakatar da ziyarar da manyan jakadun kasar suka shirya kaiwa Amurka a wani bangare na nuna fushin sa kan amince da bada umarnin tsagaita wuta a Gaza. © Evelyn Hockstein / Reuters
Talla

Wannan na zuwa ne bayan da dukkannin kasashe mambobin kwamitin suka amince da tsagaita wuta, duk da yadda Amurka ta rika amfani da karfinta wajen hana hakan yiwuwa a baya.

Kwamitin wanda ya amince da tsagaita wuta cikin azumin watan Ramadan da al'ummar Musulmi ke yi a halin yanzu, ya bukaci Hamas ta yi gaggawar sakin dukakkanin 'yan Isra'ila da take rike da su.

Netanyahu ya ce, bada kan da Amurka ta yi kan wancan mataki da kwamitin ya dauka, alama ce ta nuna ja bayanta, a ci gaba da mara wa Israel'ila bayan da ta ke yi wajen kubutar da mutane 130 da Hamas ta yi garkuwa da su.

Sai dai kakakin fadar White House John Kirby ya shaida wa manema labarai cewar, daukar wannan mataki ba zai sauya komai kan manufarsu.

Kawo yanzu yakin da ake tafkawa a Gaza ya yi ajalin mutane dubu 32 tare da jikkata wasu dubu 74, kamar yadda Ma'aikatar Lafiyar Gaza ta sanar, tana mai cewa kaso biyu cikin uku na wannan adadi mata da kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.