Isa ga babban shafi

Kotun Birtaniya ta jinkirta mayar da Assange Amurka kan tuhumar leken asiri

A Talatar nan ce wata kotun Birtaniya ta yanke hukuncin cewa ba za a iya mika Julian Assange ga hukumomin Amurka ba a yanzu, wanda hakan ya ba shi nasara a wani bangaren tuhumar da aka dade ana masa kan wani labarin da ya wallafa na fallasa sirrin Amurka, lamarin da ya sa ta zarge shi da aikata mata leken asiri.

Kotun Burtaniya ta yanke hukuncin cewa ba za a iya mika Julian Assange ga hukumomin Amurka ba.
Kotun Burtaniya ta yanke hukuncin cewa ba za a iya mika Julian Assange ga hukumomin Amurka ba. AP - Matt Dunham
Talla

Biyu daga cikin alkalan kotun sun ce za su bai wa Assange wata damar daukaka kara, sai idan har a cikin makwanni uku masu zuwa hukumomin Amurka sun bada gamsassun bayanan da ake bukata na tabbatar da ba za su yanke masa hukuncin kisa ba.

Daukar wannan mataki da kotun ta yi, ya nuna cewar za a ci gaba da shari'ar da aka kwashe sama da shekaru 10 ana yi, sannan kuma Assenge zai ci gaba da zama a gidan yari na Belmarsh da ke birnin London, inda ya kwashe sama da shekaru biyar to tsare.

Masu shari'a Victoria Sharp da kuma Jeremy Johnson sun ce idan Amurka ba ta mika bayanan ba, za su ba Assange damar daukaka kara a kan keta 'yancin fadin albarkacin baki da aka yi masa.

Idan sun turo abin da ake bukata to za mu bai wa bangarorin damar yin karin bayani kafin mu yanke hukunci na karshe game da neman izinin daukaka kara.

Alkalan sun kuma tsaida ranar 20 ga watan Mayu wannan shekarar, don sauraron karar idan har Amurka ta mika dukkanin bayanan da ake bukata.

Stella Assange mai dakin Julian Assange.
Stella Assange mai dakin Julian Assange. AP - Jonathan Brady

Mai dakin Assange, Stella Assage ta ce ana tuhumar mijinta ne don kawai ya fallasa irin cin zarafin dan adama da ake yi Iraq da Afghanistan, don haka ta bukaci gwamnatin Biden ta dakatar da wannan tuhuma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.