Isa ga babban shafi

Wani jirgin ruwa yayi hatsari a gadar Scott Key da ke Baltimore na Amurka

Wani jirgin ruwa dauke da kwantenoni ya bugi gadar Francis Scott Key da ke yankin Baltimore na kasar Amurka mai tsawon kilomita 2.57 da sanyin safiyar Talatar nan, lamarin da yayi sanadiyar rushewarta da kuma batar mutane 7 a cikin ruwa.

Yadda hatsarin jirgin ruwa ya lalata gasar Francis Scott Key.
Yadda hatsarin jirgin ruwa ya lalata gasar Francis Scott Key. via REUTERS - HARFORD COUNTY MD FIRE & EMS
Talla

Jami’an hukumar kwana-kwana na yankin sun bayyana lamarin a matsayin babbar barna, sannan kuma suna nan suna ci gaba da laluben mutane 7 da suka bace a cikin ruwa.

Mun samu kira  da dama da misalin karfe 1:30 na dare, kan hadarin da wani jirgin ruwa ya yi a gadar Francis Scott Key da ke Baltimore, lamarin da ya yi sanadin rushewar.

 

Suma jami’an ‘yan sandan Baltimore sun ce an sanar da su faruwar lamarin ne da misalin karfe 1:35 kimanin karfe 5:35 ke nan agogon GMT.

Rahotanni sun nuna cewa ababen hawa da dama ne dai suka fada cikin ruwa bayan faruwar lamarin.

A shekarar 1977 ne aka samar da gadar da aka sanyawa sunan Francis Scott Key, 

Yadda gadar Francis Scott Key ta ke kafin hadarin jirgin ruwan.
Yadda gadar Francis Scott Key ta ke kafin hadarin jirgin ruwan. © Maryland Transportation Authority (MDTA) / Facebook

The bridge, named after Francis Scott Key, author of the Star Spangled Banner, opened in 1977.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.