Isa ga babban shafi

Faransa za ta tura karin jami'an tsaro dubu 4 don tabbatar da tsaro kafin Olympics

Faraministan Faransa Gabriel Attal ya ce za su kara tsaurara matakan tsaro tare da tura karin sojoji akalla dubu 4 nan da kwanaki masu zuwa don tabbatar da tsaro a fadin kasar da ke shirin karbar bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta Olympics nan da watanni 4 masu zuwa.

Firaministan Faransa Gabriel Attal ya ce za su kara tsaurara matakan tsaro tare da tura karin sojoji akalla dubu 4 don tabbatar da tsaro a fadin kasar.
Firaministan Faransa Gabriel Attal ya ce za su kara tsaurara matakan tsaro tare da tura karin sojoji akalla dubu 4 don tabbatar da tsaro a fadin kasar. AFP - BERTRAND GUAY
Talla

Wannan makakin ya biyo bayan rahoton da aka fitar a ranar Lahadi, da ya bayyana karin barazanar fuskantar hare-haren ta'addancina kasar, sakamakon kazamin harin da aka kai birnin Moscow wanda kungiyar IS ta dauki alhakinsa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

A ranar Litinin din da ta gabata shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa kungiyar IS da ta dauki alhakin kai harin Moscow kuma take da rassa a Afghanistan da kuma Pakistan, na shirin kai wa Faransa hari.

A cewar Ministan Kula da Harkokin Cikin Gidan Faransa Gerald Darmanin, maharan na son kai hari ne a lokacin da ake gudanar da gasar Olympics.

Ya ce ‘yan sandan Faransa da Jandarmomi da kuma jami’an binciken sirrin kasar, za su kasance cikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci, don tabbatar da tsaro.

Ministan ya ce daga cikin matakan da suke dauka, jami’an tsaron kasar za su tantance miliyoyin mutanen da za su halarci gasar Olympics da kuma mazauna kusa da wuraren da za a gudanar da wasannin gasar.

Rabon da Faransa ta kasance cikin shirin ko-ta -wana kan harin ta’addanci tun a watan Oktoban bara, lokacin da wani da ake zargin mai tsatsauran ra’ayin addinin Islama ya kai hari wata makaranta da ke Arewacin kasar, inda ya daba wa wani malami wuka da ya yi sanadiyar mutuwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.