Isa ga babban shafi

Faransa ta sha alwashin kawo karshen hare-haren da ake kai wa matasa

Gwamnatin Faransa na duba yuwuwar yadda za a kawo karshen hare-haren da ke faruwa a tsakanin matasa, bayan cakawa wani dan shekara 15 wuka da wani matashi ya yi a karshen mako, daya daga cikin jerin hare-haren da ya girgiza al’ummar kasar.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron kenan
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron kenan AP - Ludovic Marin
Talla

Firaministan Faransa Gabriel Attal ya shirya tarurrukan da jam'iyyun siyasa kan yadda za a tunkari wannan matsala da ke neman wuce gona da iri.

Kasar Faransa dai ta fuskanci jerin hare-hare kan matasa daga takwarorinsu a 'yan makonnin nan, inda masu tsatsauran ra'ayi da masu ra'ayin mazan jiya suka danganta wannan matsala da manufofin gwamnati na sassauta sha’anin shige da fice.

A harin baya-bayan nan, an kashe wani matashi dan shekara 15 a wani artabu da aka yi a garin Chateauroux da ke tsakiyar kasar Faransa ranar Asabar.

Ko da yake an tsare matashin tare da mahaifiyarsa mai shekaru 37, inda za a gurfanar da su gaban kotu nan da ‘yan kwanaki.

Masu gabatar da kara na zargin mahaifiyar matashin da ya aikata danyen aiki da hannu a ciki.

A farkon wannan watan, firaminista Attal, ya ba da sanarwar daukar wasu matakai na murkushe tashe-tashen hankulan matasa a makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.