Isa ga babban shafi

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aikin sake gina Gaza zai laƙume dala biliyan 40

Hukumar bunƙasa ƙasashe ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa sake gina Gaza da yaƙi ya ɗaiɗaita zai laƙume kuɗi da ya kai dalar Amuka biliyan 30 zuwa 40, kuma zai buƙaci hoɓɓasa irin wanda ba a taɓa gani ba tun bayan yaƙin duniya na 2.

Magatakardar Majalisar Ɗinkin Duniya  Antonio Guterres.
Magatakardar Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres. AP - Gian Ehrenzeller
Talla

Mataimakin magatakardan Majalisar Ɗinkin Duniya, Abdallah al-Dardari ne ya bayyana haaka a Amman, babban birnin ƙasar Jordan a wannan Alhamis.

Ya ƙara da cewa idan aikin za a yi babu ha’inci, yana iya daukar gwamman shekaru kafin a kammala, kuma ba zai kyautu Falasdinawa su yi irin wannan jira ba.

Al-Dardari ya ce yana da matuƙar mahimmanci a sake tsugunar da al’ummar  Gaza da hare-haren Isra’ila ya ɗaiɗaita a gidaje na mutunci, tare da dawo da al’amuran rayuwarsu kamar yadda suke a da.

Ya kuma yi ƙiyasin cewa an samu ɓaraguzan gidajen da suka ruguje a Gaza da ya kai tan kusan 40, yana mai cewa adadin na ƙaruwa kullayaumin.

Kashi 72 na gidajen al’umma a zirin Gaza sun rushe sakamakon luguden wuta da Isra’ila ta ke ci gaba da yi a yankin, wanda ke zuwa a matsayin martani ga harin da Hamas ta kai mata aranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.