Isa ga babban shafi
Ranar ƴan jarida ta Duniya

Ranar ƴan jarida ta duniya: Aikin jarida a yanayi na ƙalubale iri-iri

A kowacce ranar 3 ga watan Mayu ne Majalisar Dinkin Duniya ke gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan Jarida ta Duniya, bikin da ke gudana da nufin samar da cikakken ‘yancin tofa albarkacin baki a aikin na jarida, sai dai a wannan karon ranar na zuwa a dai dai lokacin da tarin ‘yan jarida ke fuskantar tarnaki a ayyukansu.

Yau ake bikin ranar ƴan jarida ta duniya.
Yau ake bikin ranar ƴan jarida ta duniya. © AFP - CHRISTOPHE ARCHAMBAULT
Talla

Bisa al’ada hukumar UNESCO ke jagorantar gudnar da bikin ranar a kowace shekara tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da fara gudanar da bikin ranar a shekarar 1993 da nufin bai wa ‘yan jarida cikakkiyar damar samun bayanai da kuma yaɗa su, baya ga samun damar iya sharhi ko tofa albarkacin baki kan dukkanin lamurra ba tare da nuna musu tsangwama ko ƙyara ba baya ga bai wa ma’aikatan na jarida cikakkiyar kariya daga dukkan barazana ko hare-hare.

Kamar kowacce shekara a wannan karon ma hukumar ta UNESCO ita ke gudanar da bikin ranar da hadin gwiwar gwamnatin Chile a birnin Santiago, yayin da gangamin bikin ranar ke gudana a fiye da kasashe 100.

Taken ranar a bana shi ne halin da aikin jarida ke ciki a wani yanayi da Duniya ke fuskantar tarnaki ta fuskar yaki da dumamar yanayi, lamarin da ya sanya hukumar ta UNESCO nanata kiran ganin ‘yan jaridan sun jajirce wajen isar da sakwannin don magance matsalolin da suka dabaibaye duniya.

A nata bangaren kungiyar tarayyar Turai ya bayyana bikin ranar ‘yancin ‘yan jaridan ta bana a matsayin mai cike da tarnaki, lura da yadda kasashe fiye da 60 ke gudanar da zabuka wanda ya sanya aikin jarida a tsaka mai wuya.

Sanarwar da UNESCO ta fitar game da ranar, ta ce wajibi ne gwamnatocin kasashe su bayar da cikakkiyar kariya ga ‘yan jarida don kauce wa kai musu hare-hare musamman a bakin aiki tare da basu damar gudanar da ayyukansu a lumana, yayin da hukumar ta yi tir da kai hare-hare kan ‘yan jaridar wadanda da dama kan rasa rayukansu a bakin aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.