Wakilai 160 ne za su halarci taron zaman lafiya kan Ukraine a Switzerland
Ma’aikatar harkokin wajen Switzerland ta ce ƙasar ta gayyaci sama da wakilai 160 zuwa taron laluɓo zaman lafiya a Ukraine, sai dai Rasha ba ta cikin su.
Wallafawa ranar:
Rasha, wadda ta ƙaddamar da mamaya a kan Ukraine a watan Fabarairun shekarar 2022 ta yi watsi da taron, inda ta ke cewa Amurka ce ta shirya shi.
Ta sha nanata cewa ba za ta shiga wata tattaunawa a geme da wannan batu ba har sai Ukraine ta amince da ƙarbe aƙalla kashi 20 na ƙasarta da ta mamaye a halin yanzu.
Ya zuwa yanzu, babu wata masaniya a game da ko shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky da na Amurka Joe Biden za su samu halartar taron.
Wani lamarin da ake shakku a kai shine ko babbar aminiyar Rasha, wato China za ta samu halartar taron.
Ko da sau ɗaya, China ba ta taɓa caccakar Rasha a game da mamayar Ukraine da ta yi ba, kana ana zargin ta da mara wa Rasha baya a kan yaƙin.
Taron, wanda zai gudana a ƙarshen mako zai kasance ne daga ranar 15 zuwa 16 na watan Yuni a birnin Lucerne na ƙasar Switzerland.
Za a wallafa sunayen ƙasashen da za su halarci wannan taro nan gaba kaɗan, sai dai abin da ake da tabbaci a kai shine za a samu wakilci da kowace nahiya, da kuma kungiyoyin G7, G20 da BRICS.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu